Satar fasaha ce babbar matsalarmu - Ali Nuhu

Hakkin mallakar hoto ali nuhu facebook
Image caption Ali Nuhu shahararren dan wasan fina-finan Hausa

Masu shirya fina-finan Hausa na Kannywood, sun yi kira ga shugaban Najeriya mai jiran gado, Muhammadu Buhari da ya tallafa musu wajen shawo kan matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya.

Fitaccen jarumin nan na fina-finan Hausa Ali Nuhu ne ya shaida wa BBC cewa matsalar satar fasaha ita ce babbar matsalar da ke addabar sana'ar tasu.

Ya yi kira ga shugaba mai jiran gado, Muhammad Buhari da ya taimaka wajen bujuro da wata doka da za ta kawo karshen halayyar.

Sai dai kuma jarumin ya amince da cewa akwai bara-gurbi a cikin masu shirya fina-finan wadanda suke taimakawa wajen aiwatar da satar fasahar.