Za a sanar da wadda ta lashe gwarzuwar 'yar kwallo

Nan da wasu 'yan sa'o'i ne za a sanar da wacce ta lashe lambar gwarzuwar 'yar kwallon kafar mata ta duniya wadda BBC za ta karrama a bana.

Za a fitar da sanarwar ne a shirin "Have your Say" na Ingilishi da ake gabatar wa a BBC da misalin karfe 3.15 agogon Najeriya da Nijar.

Wannan dai shi ne karon farko da BBC za ta fara karrama 'yar kwallon kafar da ta fi yin fice a wasa a duniya.

Za a zabi gwarzuwar daga cikin 'yan wasa biyar da suka hada da Asisat Oshoala ta Najeriya da Veronica Boquete ta Spaniya da Nadine Kessler ta Jamus da Kim Little ta Scotland da kuma Marta ta Brazil .