Gwamnatin Burundi na neman tallafi saboda zabe

Image caption Zaben Burundi

Gwamnatin Burundi ta yi kira ga jama'ar kasar da su bayar da gudunmawa domin taimakawa zaben da ake cece-kuce a kansa wanda za'a yi a watan Yuni.

An shafe makwanni ana tashe-tashen hankula a kasar an kuma yi kokarin yi wa Shugaba Pierre Nkurunziza juyin mulki wanda bai yi tasiri ba sakamakon yunkurin yin tazarce a karo na uku.

A shafinsa na na facebook -- ofishin shugaban kasar ya nemi tallafi daga wajen masu kishin kasa domin karfafa demokaradiya a kasar.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta rike wasu kudade sama da dala miliyan biyu da aka tanadar domin zaben.