Za a tallafawa Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Image caption An shafe kusan shekaru biyu ana yaki a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Kungiyoyin bayar da agaji na duniya da ke yin taro ranar Talata a Brasels, za su tattauna kan taimakon kudi da za a bai wa Jumhuriyar Tsakiyar Afrika.

Hakan ya biyo bayan sa hannun da kungiyoyin sojojin sa kai suka yi kan yarjejeniyar sulhu a kan batun ajiye makamansu tare da sake maido tsoffin mayakan cikin al'umma.

Kungiyar bayar da agaji ta "Save the Children" tana amfani da wannan dama domin jawo hankalin jama'a ga bukatun da yara ke da su bayan shafe shekaru ana zaman dar-dar.

Kungiyar tace yara da dama na fuskantar matsaloli na kaduwa da firgita sakamakon abinda suka gani ko kuma cin zarafin da aka yi musu yayin yakin.