Mahaukaciyar guguwa ta yi barna a Mexico

Image caption Karfin iskar ya kifar da wata motar bas dauke da fasinjoji

Wata mahaukaciyar guguwa tare da ruwan sama a yankin kudu maso yammacin Amurka da arewacin Mexico sun hallaka akalla mutane goma 19.

Yawancin mutanen da suka mutu a birnin Acuna ne inda ta wajen ne mahaukaciyar guguwar ta ratsa.

Wakiliyar BBC da ke yankin ta ce, mahaukaciyar guguwar da ta ratsa cikin dakikoki 6 kacal ta rinka wurga motocin mutane sama, wasu ma iskar ta buga su jikin gine-gine a dai-dai lokacin da suke kokarin tafiya wajen aiki da makaranta.

A Texas kuma rahotanni sun ce mutane 3 ne suka mutu - yayinda ake fargabar bacewar wasu mutanen 12 bayan ambaliyar ruwa ta yi awon-gaba da wani gida na yawon shakatawa.

Gwamnan Texas ya ce wannan mummunar ambaliya ce da bai taba ganin irinta ba.