An yi rashin shahararren masanin Lissafi

Zarumai a fim din Oscar Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Zarumai a fim din Oscar

Masanin lissafin nan John Nash wanda ya yi sanadiyyar hada fim din nan da ya lashe kyautar Oscar watau "A beautiful Mind" ya mutu a wani hadarin mota da Uwargidansa, a cewar 'yan sanda.

Nash, mai shekaru 86 da Uwargidansa mai shekaru 82 Alicia sun rasa ransu ne lokacinda Taxi din su ta yi hadari a New Jersy kamar yadda 'yan sandan suka fada.

Masanin lissafin, ya shahara wajen wani lissafi da ya kirkira mai suna "game theory" wanda ya cinye kyautar yabo ta masana tattalin arziki a 1994.

Nasarorin da ya samu ne a lissafi da gwagwarmayar da ya yi ta ciwon lissafin lamurra da yawanci ya kan shafi tsoffi - shine alkiblar fim din da aka yi a shekara ta 2001.

Russell Crowe wanda ya yi shiga irin ta sa a fim din ya aike da sako ta twitter cewar "wannan mutuwa ta sanya ni na rasa ta cewa". A gaskiya ina juyayin mutuwar John da Alicia, ina kuma ta'aziyya ga iyalinsu.

Daraktan fim din Ron Howard shi ma ya aike da sakon twitter yana cewar ina juyayin mutuwar "masani" John Nash da Uwargidansa.

Alicia Nash ta taimaka wajen kula da mai gidan ta, kuma daga bisani dukkansu biyu suka zamo shahararru wajen sha'anin lafiyar kwakwalwa.

An watso Nash din ne da Uwargidansa a waje daga cikin motar kamar yadda 'yan sanda suka fada.

Rahotannin kafofin watsa labarai sun ce Mutanen biyu mai yiwuwa ba su daura bell din daure jiki a mota watau seat belt.

Karin bayani