An kalubalanci Buhari kan cin zarafin bil adama

Image caption 'Yan Najeriya da dama na cikin halin tagayyara sakamakon rikice-rikice a kasar

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga shugaban Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari da ya yi gaggawar magance matsalolin cin zarafin bil'adama da rikice-rikice da ake fama da su a kasar.

Wani mai bincike na kungiyar Mausi Segun, ya ce suna bukatar Buhari ya cika alkawuran da ya dauka na magance matsalolin da 'yan Najeriya ke fuskanta a kowacce rana da zarar an rantsar da shi.

"Dole shugaba mai jiran gado da gwamnatinsa su yi kokarin dawo da 'yanci da martabar dan adam a Najeriya," in ji Mr Segun.

Tun dawowar mulkin dimokradiyya a Najeriya a shekara ta 1999 dai, fiye da farar hula 20,000 aka kashe a rikice-rikicen kabilanci da siyasa da na ta'addanci, yayin da kusan mutane miliyan 1.5 kuma suka bar muhallansu.

Zababben shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi alkawarin magance dumbin matsalolin 'yan kasar idan ya dare mulkin kasar lokacin da yake yakin neman zabensa.