Jami'an tsaro sun cafke jami'an FIFA

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tunanin tisa keyar jami'an Fifa zuwa Amurka

'Yan sanda a birnin Zurich na kasar Suwizalan sun kama jami'an hukumar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA, domin kai su kasar Amurka su fuskanci hukunci bisa zargin cin hanci da rashawa.

Wannan al'amari yana zuwa ne a dai-dai lokacin da shugabannin FIFA suke halartar taron hukumar na shekara-shekara a birnin, a inda kuma ake sa ran shugaban hukumar, Sepp Blatter zai ayyana niyyarsa ta neman shugabancin hukumar karo na biyar, a ranar Juma'a.

Ana dai zargin su da almundahana a gasar wasannin cin kofin duniya da tallata su da kuma watsa su ta kafafen yada labarai, a tsawon shekaru 20.

Amma wasu na ganin cewa an yi hakan ne domin dusashe tauraron shugaban hukumar ta FIFA, Sepp Blatter, dangane da aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin hukumar karo biyar.