"Ana korar kananan sojoji daga aiki"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kananan sojoji a Najeriya sun ce ana sallamar su ba bisa ka'ida ba

Wasu kananan sojoji a Najeriya sun yi ikirarin cewa ana sallamar su daga aikinsu, kuma mai yiwuwa a sallami karin wasu a nan gaba.

Sojojin dai sun yi zargin cewa hukumomin sojin kasar na sallamar wasun su daga aikin soji bisa zargin su da rashin tunkarar mayakan kungiyar Boko Haram a fagen daga a lokacin da 'yan Boko Haram suka kwace garin Mubi, a watan Nuwambar shekarar da ta gabata.

Wani soja wanda ya nemi BBC ta sakaya sunansa saboda sha'anin tsaro, ya fadi cewa ana korar su ba tare da an ba su komai ba.

Sai dai kuma sojojin sun yi kira ga shugaban kasa mai jiran gado, Muhammadu Buhari da ya sake yin duba ga matakin da hukumar sojin ta dauka na korar su daga aiki.