"Ba a mutunta Musulmai a duniya"

Image caption Sheikha Moza da wasu daga cikin mahalarta taron a jami'ar Oxford

Wata babba a gidan sarautar Qatar ta yi gargadi a kan cewar ana cin zarafin musulmai ta hanyar yada matsananciyar tashin hankali a gabas ta tsakiya.

A lokacin da take gabatar da wani jawabi a jami'ar Oxford, Shiekha Moza bint Nasser ta saka ayar tambaya a kan ko "Me ya sa ba'a damu da rayuwar musulmai ba kamar yadda aka damu da na wasu?"

Ta ce banbance-banbance tsakanin gabas da yamma yana haifar da "tsoro da mummunan zato a kan dukkanin abubuwan da suka shafi musulunci".

Sheikha Moza ta kara gargadi a kan "takurawa" a kasashen Larabawa.

Sheikha Moza, mata ce, wacce ake gani da daraja da kima a gabas ta tsakiya, ta kara yi wa masu sauraro bayani a lokacin da take jawabi a kan illar kyamar kasashen yamma.

Ta kara da cewar, kuma gazawar ci gaba a siyasar gabas ta tsakiya, shi ya sa ake yi wa musulunci munmunar fassara.

'Kin jinin musulunci'

Sheikha Moza ta yi gargadi a lokacin da ake bude wani sabon gini a gabas ta tsakiya a kwalejin Anthony, inda ta ce yayin da kasashen yamma suka zaku da su fahimci musulunci, Musulmai suna ci gaba da fuskantar rashin yadda.

Ta bayyana hakan a matsayin bambanci tsakanin kin musulunci da kyamar Musulmai.

Kuma ta dasa alamar tambaya a kan ko yunkurin da ake yi na dunkulewar al'ummar duniya wuri guda watau globalisation na tasiri ko cimma manufar ta?

Image caption Ana kyamar musulmai a duniya

Tashin farko ana kallon musulmi a matsayin musulmi a maimakon dan adam.

Mahaifiyar sarkin Qatar din ta kara da cewar wannan kallon da ake yi wa musulmai abu ne "mai ban tsoro kuma wanda ba'a sani ba".

Sheikha Moza wadda babbar 'yar siyasa ce a kasashen yankin gulf mai arzikin man fetur da iskar gas, ta ce abin da ya biyo bayan hakan yana da fuska biyu idan lamarin ya shafi rikici.

Ta kalubalanci yawan amfanin da kalamar "medieval" wato " na da" da ake yi wajen bayyana abubuwan da masu tsatstsauran ra'ayi na gabas ta tsakiya suka aikata.

Sheikha Moza ta ce "kafafen yada labarai na duniya wadanda suka hada da na kasashen yamma da kuma kasashen Larabawa, suna yawan ikirarin cewar musulunci bai yarda da 'yancin fadin albarkacin baki ba.