Nigeria za ta kori wasu 'yan China a Kano

Image caption Marina sun ce 'yan China na kashe musu kasuwa

Hukumomi a Nigeria za su kori 'yan China biyar daga cikin kasar bisa zargin fasa-kwaurin kayayyaki zuwa Kano.

Jami'an kwastam da na hukumar kula da shige da fice a Nigeria, sun ce 'yan Chinar ba su da izinin takardar zama a kasar, balle izinin gudanar da kasuwanci a cikin kasar.

Kakakin hukumar kwastam, Wale Adeniyi ya ce "Mutanen 'yan China su biyar su ne ke shigo kayayyakin masaku zuwa Kano ta barauniyar hanya."

A farkon wannan watan ne jami'an kwasman suka damke 'yan kasar ta China bisa zarginsu da yin kasuwanci a Kano ba tare da izini ba.

A kwanakin baya ne, daruruwa marina a Kano suka yi zanga-zanga a kan cewar 'yan China na kashe musu kasuwa abin da ke barazana ga marina kusan 30,000 a jihar.

Marina na zargin 'yan China na shigowa da jabun kayayyaki masu saukin kudi da ke hanasu cikin kasuwarsu da suka gada shekara da shekaru.