Adesina ya zama sabon shugaban AfDB

Hakkin mallakar hoto bb
Image caption Dr Adesina ya doke mutane bakwai a takarar

Ministan harkokin ayyukan gona a Nigeria, Akinwumi Adesina ya zama sabon shugaban bankin bunkasa Afrika watau ADB.

Dr Adesina ya lashe zaben ne bayan da ya yi nasara a kan 'yan takara bakwai da ya fafata da su a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast.

Sai da aka yi zabe har zuwa zagaye na bakwai kafin Adesina ya samu nasarar lashe zaben.

Dr Adesina zai maye gurbin Donald Kaberuka a matsayin shugaban bankin daga ranar daya ga watan Satumbar bana.

An kafa bankin ADB ne a shekarar 1964 domin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika da kuma rage talauci a tsakanin al'umma.