Sai mun tumbuke Assad —Alka'ida

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane na cikin mawuyacin hali a Syria

Jagoran sojojin sa kai na kungiyar Al-Ka'ida a Syria ya ce burin kungiyarsa shi ne su kame birnin Damaskus tare kuma da tumbuke shugaba Assad.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al-Jazeera, Abu Mohammed al-Golani, wanda ya ke jagorantar kungiyar Nusrah Front, ya gargadi 'yan kabilar Alawi wadda ita ce kabilar shugaba Assad da su juya wa shugaban da mulkinsa baya.

Ya kuma ce kungiyarsa ba ta da niyyar kai wa kasashen yamma hari kuma ba ta yaki da Kiristoci.

Kungiyar Nusra Front ita ce mafi karfi daga cikin kungiyoyin masu da'awar jihadi wadda ta samu galaba a kan dakarun gwamnati a 'yan makonnin da suka gabata.

Rikicin Syria ya janyo mutuwar dubun dubatan mutane a kasar.