'Yan takarar bankin AFDB

Image caption 'Yan takarar Bankin Afrika, AFDB.

Birima Sidibe, daga Mali

Birama Sidibe, Injiniya ne wanda ya kware a fannin ban ruwa.

Ya yi aiki a sashen ci gaban kasa, na tsawon shekaru sama da 30 kawo yanzu.

Ya yi aiki tare da bankin bunkasa Afrika daga shekara 1983 zuwa 2006.

Birama Sidibe ya kuma yi aiki da bankin bunkasa kasashe Musulmi da kamfanin Shelter-Afrique da ke Nairobi, da kuma kamfanin River Organization da ke Senegal.

Jelloul Ayed, daga Tunisia

Jelloul Ayed, na da shekaru 64 kuma shahararren ma'aikacin banki ne a kasarsa.

Ma'aikacin, kwararre ne taimakawa wajen kafa kamfanoni a kasashen Tunisia da Morocco ta hanyar wani asusun kudi na kasuwaci a Turai.

A shekara ta 2011, a matsayinsa na ministan kudi a gwamnatin rikon kwarya bayan kifar da shugaba Ben Ali, ya gabatar da tsarin ci gaban da kasarsa a taron kasashe takwas masu karfin tattalin arziki watau G8 summit.

Bedourma Kordje, daga Chadi

Wannan shi ne Ministan kudin Chadi a yanzu.

Bedourma Kordje, Injiniya ne na fannin sadarwa kuma ya shafe shekara 29 a bankin bunkasa Afrika watau Africa Development Bank kafin ya zama Ministan kudin Chadi a shekara 2012.

Shugaban Chadi Idriss Deby, na kamun kafa wajen mambobin taron kasashen Afrika ta tsakiya da su goyi bayan Bedourma Kordje a zaben da za'ayi na AFDB.

Cristina Duarte, daga Cape Verde

Ita ce kade macce a yakin neman zaben, amma ba zama ta macce ne kadai kadarinta ba.

Cristina Duarte ta bukaci a zabe ta saboda cancanta ba don zamanta macce ba.

Ita ce Ministar kudi a kasarta tun shekarar 2006.

Ana yabonta wajen jawo bunkasar tattalin arzikin kasar Cape Verde.

Cristina Duarte ta yi wa kungiyoyin ci gaban kasa da kasa aiki da dama.

Adesina Akinwunmi, daga Nigeria

Shi ne Ministan ayyukan gona da ci gaban karkara na yanzu a Najeriya.

Dan shekaru 55 , kuma a baya shi ne mataimakin shugaban kamfanin Alliance for a Green Revolution (AGRA).

Yana da digirin digirgir a fannin tattalin arzikin noma.

Mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin gwarzon Afrika a shekarar 2013 saboda gyaran da ya kawo fannin noma.

Sufian Ahmed, daga Habasha

Sufian Ahmed na da shekaru 57, shi ne Ministan kudi da ci gaban tattalin arziki, kuma yana so ya yi amfani da bunkasar tattalin arzikin kasarsa a matsayin hujjar a zabe shi

Ya samu yabo sosai a kan gudumuwar da ya bada wurin nasarar tattalin arzikin da kasar ta samu.

A baya ya yi kwamishinan hukumar hana fasa-kwauri watau kwastan, duk a lokacin karatunsa, ya samu nasara sosai.

Samura Kamara, daga Saliyo

Masanin tattalin arziki ne, kuma a baya ya yi aiki da hukumar bada lamuni ta duniya watau IMF, amma yanzu shi ne ministan harkokin waje da hadin kan kasashe.

A dalilin haka ne, ya sa Shugaban kasar Ernest Bay Koroma ya nemi a ba shi matsayi a gwamnatinsa.

A baya kuma ya yi ministan kudi, inda ya yi fice a yakin neman hadin kan Afrika.

Thomas Sakala, daga Zimbabwe

Kungiyar kasashen kudancin Afrika- SADC ta zabi wannan dan kasar Zimbabwe din dan takararta.

Ya yi ritaya daga bankin bunkasa Afrika a bara, kuma matsayinsa na dan cikin gida zai kara masa tagomashi

Ya yi ayyuka tare da gwamnatocin Afrika da dama. Mr Sakala ya fi mayar da hankali ne a kan yadda za a yi ayyukan gina kasashen Afrika.