FIFA: Warner ya shiga hannun jami'an tsaro

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zarge zargen cin hanci sun dabaibaye hukumar FIFA

Tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Jack Warner, ya shafe daren Laraba a kurkuku a kasar Trinidad da Tobago, bayan da Amurka ta zarge shi da aikata cin hanci da rashawa

Masu gabatar da kara Amurkawa sun zargi Mr Warner da hannu a biyan wasu kudade da jami'an hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu suka yi, na fiye da dala miliyan 10 a matsayin cin hanci domin a bai wa kasar damar karbar bakuncin gasar kwallon kafar duniya a shekarar 2010.

Mr Warner da kuma Hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudun sun musanta wannan zargi.

Bayan wannan zargin ne kuma, Mr Warner ya mika kansa ga 'yan sanda.