"A yi bincike ban da bita-da-kulli"

Muhammadu Buhari mai jiran gado da shugaba Jonathan mai barin gado

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Muhammadu Buhari mai jiran gado da shugaba Jonathan mai barin gado

Shugaban Najeriya mai barin gado Goodluck Jonathan, ya shawarci shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari da kada ya ware gwamnatinsa kadai idan har zai yi bincike.

Ya ce dukkan masu bai wa Buhari shawara cewa ya binciki gwamnatinsa, to kamata ya yi su bashi shawara ya binciki dukkan gwamnatocin da suka gabata in ba haka ba lamarin zai zamo tamkar bita-da-kulli za a yi masa.

Jonathan ya bayyana hakan ne a yayin da yake zaman karshe na taron majalisar ministocinsa a ranar Laraba.

Shugaban mai barin gado ya ce, "Wasu mutanen na ta ihun a binciki gwamnatin nan. Ni kuwa na san cewa a Najeriya akwai abubuwa da yawa da ya kamata a bincika."

"Kamata ya yi a binciki basussukan da ake bin jihohin kasar nan ma tun daga shekeara ta 1960 har zuwa yau. Amma sai ake ta yayata cewa gwamnatin Jonathan ce ta ciyo dukkan bashin," in ji shugaban kasar.

A baya-bayan nan ne dai mutane da dama a kasar suke ta kira ga Muhammadu Buhari da ya tabbatar ya bincika gwamnatin Goodluck Jonathan.