Adesina na takarar shugabancin AfDB

Hakkin mallakar hoto bb
Image caption Mr AKinwumi Adesina tsohon Ministan noma da raya karkara na Najeriya

A ranar Alhamis ne hukumar gudanarwa ta gwamnonin bankin raya kasashen Afrika za ta zabi sabon shugabanta.

Za a zabi sabon shugaban bankin ne daga cikin 'yan takara 8 da wani kwamitin hukumar gwamnonin ya tantance su a ranar 11 ga watan Fabrairu.

Daga cikin 'yan takarar akwai mutane 4 daga kasashen Yammacin Afrika, da suka hada da Ministan ayyukan Gona na Najeriya Mr Akinwumi Adesina, wanda wa'adinsa ya kare a ranar Laraba.

Sabon shugaban Bankin da za a zaba a yau, zai maye gurbin Mista Donald Kaberuka.

Mannir Dan Ali, babban Edita a kamfanin Media Trust, ya shaidawa BBC cewa bankin na taka mahimmiyar rawa wajen gudanar da manyan ayyuka a kasashen Afrika da kuma taimako.

Idan har an zabi dan Najeriyar, wannan zai kasance lokaci na farko da Najeriya zata shugabanci Bankin.