Mutane 141 sun kona kansu a China tun 2009

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zangar adawa da kisan kai a Tibet ta hanyar kona kai

Wata mahaifiyar yara biyu dake zaune a arewa maso yammacin China ta bankawa kanta wuta har sai da ta kone a wani mataki na nuna adawa da mulkin Beijing a Tibet.

Kungiyoyin kare hakkin dan'adam sun ce matar -- Sangye Tso ta kona kanta ne a wajen wani ofishin 'yan sanda a lardin Gansu.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun dauke gawar matar sannan suka kai samame gidajen 'yan uwanta.

Wannan dai shi ne kashe kai ta hanyar bankama kai wuta na 141 da aka samu a Tibet da wasu wurare tun a shekarar 2009.

Sai dai hukumomin 'yan sanda sun ce lamarin kwata-kwata bai faru ba.

A makon jiya ne, wani mutum mai 'ya'ya hudu shi ma ya bankawa kansa wuta har lahira a kudu maso yammacin lardin Sichuan, inda nan ma mutanen Tibet suke da yawa.

Mutanen Tibet da yawa suna zargin gwamnatin China da gallaza musu saboda addini da kuma al'ada, domin 'yan babbar kabilar China -- Han sun mamaye wuraren da 'yan Tibet suke.