Kai Tsaye: Bikin rantsar da Buhari a Abuja

Latsa nan domin sabunta shafin

Hakkin mallakar hoto AP

Barka da zuwa shafin BBC Hausa kai tsaye a kan bikin rantsar da sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo. Da kuma wasu gwamnoni a jihohin kasar.

Za ku iya aiko mana da ra'ayoyinku ta e-mail hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta whatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

Mun gode da ziyartar wannan shafin. Sai kuma wani lokaci. Ku ci gaba da kasance da sashin Hausa na BBC.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na gaisawa da sabon shugaba Muhammadu Buhari

12:33 Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nada Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi a matsayin Sakataren gwamnatin Kano. Da ma Rabi'u Bichi shi ne Sakataren gwamnatin Kano a lokacin tsohon gwamna Kwankwaso. Sauran nade naden da Ganduje ya yi sun hada Alhaji Usman Bala Muhammad a matsayin shugaban ma'aikata, da Baba Halilu Dantiye a matsayin darakta janar na kafafen yada labarai da sadarwa. Da Ameen Yassar a matsayin sakataren watsa labarai, sai kuma Bala Salihu a matsayin mai taimakawa gwamna na musamman kan al'amuran jaridu. Wata takarda da sabon gwamnan Dr. Ganduje ya sa wa hannu ta ce nadin ya fara aiki nan take.

Image caption Janar John Atom Kpera mai ritaya a wajen rantsar da Muhammadu Buhari.

12:26 Jam'iyyar PDP wacce ta sha kaye a zaben 2015 ta fitar da sanarwa, inda ta taya sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari murnar kama mulki.

12:22 Sabon shugaban Muhammadu Buhari ya fice daga dandalin Eagle Square bayan kammala jawabinsa ga 'yan Najeriya.

12:15 Muhammadu Buhari ya kammala jawabinsa na 'yan Najeriya, inda ya sha alwashin yin bakin kokarinsa domin magance matsalolin da ke damun kasar.

Hakkin mallakar hoto NTA
Image caption Muhammadu Buhari yana shan rantsuwa.

12:01 Yanzun nan aka rantsar da sabon gwamnan jihar Enugu, Hon. Ifeanyi Lawrence Ugwuanyi a dandalin Michael Okpara da ke birnin Enugu. Ya kuma sanya hannu kan takardar rantsuwar kama aiki. In ji wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed

11:59 Sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, yabawa makwabtan kasashe kamar Jamhuriyar nijar da Chadi game da taimakawa Najeriya da suke yi wajen yaki da 'yan kungiyar Boko Haram. Ya ce zai magance matsalolin Najeriya da yardar Allah, kuma 'yan kasar za su yi alfahari.

11:55 Sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya fara jawabi ga 'yan kasar.

Image caption Miliyoyin 'yan Najeriya suna kallon jawabin sabon shugaban kasar, Muhammadu Buhari a talabijin.

11:50 Wakilinmu a Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed, ya ce yanzu haka an rantsar da mataimakiyar gwamnan jihar Enugu, Honourable Cecilia Ezilo a dandalin Michael Okpara da ke birnin Enugu. Ta sa hannu a takardar rantsuwa.

11:37 Wakilinmu na Kaduna, Nura Muhammad Rimgim, ya shaida mana cewa wasu matasa sun jefi Sarkin Zazzau, mai martaba Alhaji Shehu Idris a dandalin rantsar da sabon gwamna Nasir Elrufai. An fitar da Sarkin daga wajen bikin.Wakilin namu na ya tabbatar da cewa an ji wa mutane da dama rauni a wajen. Yanzu haka dai 'yan sanda sun fesa barkonon-tsohuwa domin dawo da doka da oda.

11:25 Sojoji suna fara faretin girmamawa ga sabon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Image caption Dandazon mutanen da suka halarci wajen rantsar da Muhammadu Buhari

11:16 Shugaba Buhari ya shiga bakar mota mai budadden baya tare da wasu sojoji domin zagaya dandalin Eagle Square yana dagawa mutane hannu da jinjina.

11:10 Sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saki fararen tantabaru wanda hakan alama ce ta zaman lafiya. Bayan haka kuma sai aka yi sojoji suka buga bindiga sau 21 da ke nuna girmamawa ga sabon shugaban kasa.

11:08 Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya bar dandalin Eagle Square.

11:05 A kaduna kuwa,Malam Nasir El-Rufai ya sha rantsuwa a matsayin gwamnan jihar, sannan mataimakinsa Bala Bantex ma ya sha rantsuwa.

Image caption Malam Nasir El-Rufa'i ya sha rantsuwar kama mulki a matsayin gwamnan jihar Kaduna

11:00 Hafsan hafsoshin Najeriya Alex Badeh ya bai wa tsohon shugaba Jonathan tutar Najeriya da ta rundunar sojin kasar inda shi kuma ya mika wa shugaba Buhari wanda hakan ke nuna ya zama Kwamandan askarawan Najeriya.

10:52 Sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan takardun rantsuwar kama mulki inda bayan nan ya daga hannayensa yana jinjanawa jama'ar da ke wannan dandali. Bayan haka kuma sai tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika wa shugaba Buhari takardun ragamar mulkin Najeriya, sai kuma suka sha hannu.

Image caption Buhari yayin da ake rantsar da shi

10:49 Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama mulki a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya karkashin jagorancin alkalin alkalai na kasa, Mahmud Muhammad.

10:45 An gayyaci shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari zuwa dandamalin da zai sha rantsuwar kama aiki.

10:42 Sabon mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya gaisa da wasu manyan baki bayan gama shan rantsuwar kama mulki a matsayin mataimakin shugaban kasa. Ya koma wajen zamansa.

10:37 Zababben mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya hau dandamalin da alkalin alkalai yake inda yake shan rantsuwar mulki gabannin zababben shugaban kasa ya sha tasa.

Hakkin mallakar hoto CHANNELS TV
Image caption Shugaba mai jiran gado da shugaba mai barin gado yayin da ake addu'ar bude taro

10:36 An gayyaci alkalin alkalai don ya hau dandamalin da zai rantsar da sabon shugaba Muhammadu Buhari.

10:33 An gabatar da babban alkalin alkalan Najeriya Muhammad Mahmud, wanda zai rantsar da sabon zababben shugaban kasa da mataimakinsa.

10:30 An bude taron rantsarwar da addu'a. Ina aka soma da na Kirista sannan aka yi na Musulmi.

10:27 An rantsar da sabon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan Kano da mataimakin sa Farfesa Hafizu Abubakar a matsayin mataimakin gwamna.

A jihar Katsina ma an rantsar da Hon. Aminu Bello Masari a matsayin sabon gwamnan Jihar Katsina.

Image caption Faretin sojoji na gaisuwar girmama baki "Guard of Honor".

10:23 Shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan ya koma wajen zamansa inda yake gaisawa da manyan baki, bayan an gama taken Najeriya.

10:19 Ana buga taken Najeriya a yanzu yayin da dukkan mutane suka mike tsaye.

10:14 Shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan ya iso dandalin Eagle Square. Nan ba da jimawa ba shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari zai sha rantsuwar mulki.

10:09 Tarihi a karon farko a Nigeria. Dan adawa zai dare kan kujerar mulki watau Muhammadu Buhari.

Image caption Isowar sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, dandalin Eagle Square

10:00 Zabbaben shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso dandalin Eagle Square tare da matarsa Aisha Buhari. Yanzu ana jiran shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan.

09:52 Mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo da kuma zababben mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo dun sun iso dandalin Eagles. Ana jiran Jonathan da Buhari.

09:49 Ana ci gaba kade-kade a dandalin Eagle Square domin nishadantar da baki masu jira, gabannin zuwan shugaba mai barin gado da shugaba mai jiran gado.

Image caption Makada da mawaka na nishadantar da manyan baki a dandalin Eagle Square

09:37 Bisa dukkan alamu a yanzu kawai ana jiran shugaban kasa mai barin gado, Goodluck Jonathan da shugaba mai jiran gado, Muhammadu Buhari domin su shigo cikin dandali kafin a soma bikin gadan-gadan, in ji Editanmu Mansur Liman

09:33 Bayan dukkan manyan baki sun iso dandalin Eagles Square, za a soma bude bikin ne da addu'a da misalin karshe 9:55 inda kuma ake saran soma rantsuwa daga karfe 10. Babban alkalin alkalan Nigeria ne zai rantsar da sabon shugaban kasar da mataimakinsa.

Image caption Manyan hafsoshin tsaron Najeriya a yayin da suke iso wa dandalin Eagle Square

09:23 Editanmu Mansur Liman ya bayyana mana cewa manyan hafsoshin tsaro a Nigeria sun iso dandalin. Shi ma tsohon shugaban mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya isa Eagles Square

09:14 Can a Kano da ke arewacin Nigeria ma an soma biki, inda 'yan siyasa ke jiran mika mulki ga sabon gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje a fadar gwamnatin Kano a yayin da Rabiu Musa Kwankwaso ya kamalla wa'adin mulkinsa.

Image caption 'Yan siyasa a Kano suna jira a mika mulki ga sabuwar gwamnati

09:09 Tsoffin shugabannin Najeriya Olusegun Obasanjo da Janar AbdulSalam Abubakar sun iso dandalin Eagle Square. Haka shi ma shugaban kasar Afrika ta Kudu Mista Jacob Zuma, ya iso filin.

09:05 'Yan Nigeria da dama a ciki da wajen kasar na bibiyar abubuwan da ke faruwa a Abuja, ta rediyo, talabijin da intanet. Kuma 'yan jarida da dama daga kasashen waje sun halarci Eagles Square domin bayyana irin wainar da ake toyawa.

Image caption Manema labarai sun yi dafifi a dandalin Eagle Square

08:58 Wannan dai shi ne zai kasance karo na biyu da za a rantsar da tsohon shugaban mulkin soja a Nigeria a matsayin shugaban farar hula, amma kuma shi ne karo na farko da za a mika mulki cikin ruwan sanyi daga hannun gwamnati mai ci zuwa ga hannun gwamnatin jam'iyyar adawa.

08:53 Shin wanene Buhari? Tsohon sojan, dogo, siriri, wanda aka haifa a garin Daura mai cike da tarihi da ke arewacin Nigeria, shekaru 72 da suka wuce.

08:49 An bai wa makada da masu wasannin al'adu na gargajiya daban-daban fili suna nishadantar da mutanen da suka riga suka hallara a wannan fili.

Image caption An ci gaba da dakon manyan baki

08:44 Wannan ne karo na biyu da Muhammadu Buhari zai jagoranci Nigeria. Saboda a shekarar 1983 an yi juyin mulkin soja inda aka hambarar da gwamnatin Alhaji Shehu Shagari sannan Buhari ya zaman shugaban mulkin sojin kasar.

08:40 Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jagora a jam'iyyar APC Alhaji Atiku Abubakar ya iso wannan dandalin na Eagle Square tare da mukarrabansa.

08:38 An yi wa dandalin Eagle a Abuja kwalliya inda ko ina aka saka launin kore da fari watau alamat tutar Nigeria

Image caption Wasu daga cikin manyan baki mata a dandalin Eagle Square

08:33 Daya daga cikin jagororin jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya iso dandalin wannan taro tare da tawagarsa.

08:31 'Yan sanda sun fara fareti na gaisuwar girmama baki da ake kira "Guard of Honor".

08:26 A yanzu haka an fara kade-kade a dandalin, kuma makadan jihar AKwa-Ibom ne suke yi.

Image caption Wajen zaman manyan baki a Eagle Square

08:21 A yanzu haka an fara gabatar da manyan bakin da suka isa wannan dandali na Eagle Square.

08:20 Sojoji kan dawakai na ta zagayawa a filin Eagle Square domin tabbatar da doka da oda.

08:19 An girke daruruwan jami'an tsaro da na Civil Defence inda sabon shugaban kasa zai sha rantsuwar kama mulki.

08:05 Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Biritaniya, Phillip Hammond na daga cikin manyan bakin da za su halarcin bikin shan rantsuwar a dandalin Eagles da ke Abuja.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun a ranar Alhamis, Shugaba Jacob Zuma na Afrika ta Kudu ya iso Abuja

08:00 Shugabannin kasashen Afrika da dama sun iso birnin Abuja tun a daren ranar Alhamis domin halartar bukin rantsar da sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari. Daga cikinsu akwai shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma da na Mali Ibrahim Boubacar Keita da kuma na Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo har da na Zimbabwe Robert Mugabe da kuma Firai Ministan Habasha, Hailemariam Desaleg.