An kai hari masallacin Shi'a a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption A makon da ya gabata ma an kai hari a wani masallacin 'yan Shi'a

Rahotanni da ke fitowa daga Saudi Arabiya na cewa an kai harin bam a wajen wani masallacin Shi'a a birnin Dammam da ke gabashin kasar.

Rahotannin da suka fito da farko sun nuna cewa harin na kunar bakin wake ne.

Ba a dai tabbatar da adadin barnar da aka yi ba.

Mako guda kenan dai-dai da aka hallaka fiye da mutane 20 a wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin mabiya Shi'a da ke wani kauye a yankin, wanda kuma kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.

Tashe-tashen hankula na karuwa a Saudiyya musamman tun bayan da kasar ta fara jagorantar rundunar hadin gwiwar soji ta kasashen Larabawa domin kai hare-haren sama a Yaman.