China ta yi watsi da bukatar daina mamaye

Image caption Daya daga cikin tsibiran tekun kudancin China

Kasar China ta yi watsi da bukatar da Amurka ta yi mata na dakatar da ci gaba da mamayen da take yi a tekun kudancin China.

Beijing din ta ce ikonta ta ke nuna wa a tekun, da kuma sauke nauyin dake kanta na kasa da kasa.

Wani kwamandan sojojin China Admiral Sun Jianguo ya shaidawa mahalarta taron kan sha'anin tsaro a Singapore cewa bukatar zaman lafiya ita ta kawo mamayen.

China ta ce ta gina tsibirai a wasu yankuna na tekun domin kyautata rayuwar dakarunta data girke a wuraren da taimakawa ga ayyukan bincike da ceto lokacin hadura a teku, da kare aukuwar bala'o'i da kuma kare muhalli.

Hukumomin China sun dage lalle kasar ita keda iko da tekun, wanda babbar hanya ce ta zirga zirgar jiragen ruwa na duniya, wanda kuma ke da albarkatun mai da gas masu yawa.

Kare manufofin China da daya daga cikin kwamandojin sojin ta ya yi game da tekun kudancin China, ya zo ne kwana daya bayan Amurka ta bukaci kasar sa data dakatar da mamayen da take yi.

A ranar Juma'a Sakataren harkokin tsaron Amurka Ash Carter ya shaida wa mahalarta taron cewa mamayen da China ta ke yi a tekun ya sabawa dokokin kasa da kasa.