'Yan Boko Haram sun harba roka a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram

A Najeriya, wasu mazauna Maiduguri na jihar Borno sun ce sun shafe daren Juma'a suna jin karar fashewar wasu abubuwa a birnin.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da kauyen Dala dake kudancin Maiduguri.

Wasu rahotannin sun ce ba ainihin bama bamai bane suka fashe, wasu irin manyan harsasai ne na RPG da ake kakkabo jirgi da su mayakan Boko Haram suka rinka harbawa a lokacin da suka kasa kutsawa garin Maiduguri..

Rahotannin sun ce mayakan Boko Haram din sun kasa shiga Maidugurin ne saboda martanin da sojoji suka mayar kan su da kuma ramuka da aka hakka a zagayen garin maiduguri.

Wani daga cikin harsasan na kakkabo jirage ya fada wani gida a kauyen Gomari dake yankin, lamarin daya yi sanadiyar mutuwar mutanen gidan.

Babu dai wata majiya ta gwamnati da ta tabbatar da hakikanin abinda ya faru zuwa wannan lokaci.