Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 13

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani dan kunar bakin wake ya tada bam a wani masallaci a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wani wanda lamarin ya faru a gabansa ya shaida wa BBC cewa akalla mutane 13 sun rasa rayukansu wasu kimanin 35 kuma sun sami raunuka.

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da aka tayar da sallar la'asar a masallacin da ke kusa da kasuwar Monday Market.

Wani wanda ya ke cikin masallacin kuma ya samu rauni a sabilin harin, ya ce sun tayar da sallah la'asar ne, sai dan kunar bakin waken ya tayar da bam.

Sabon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da wannan hari da aka kai.

A cikin wata sanarwar da ofishin yada labaransa ya bayar, Shugaba Buhari ya yi alkawalin cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da karfin ikon da take dashi wajen murkushe abin da ya kira 'ta'addanci'.

Harin na ranar Asabar dai yazo ne bayan wasu hare-haren rokoki da 'yan Boko Haram suka kai a garin na Maiduguri a ranar Juma'a da daddare, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane takwas tare da jikkita wasu da dama.

Karin bayani