Amurka ta bukaci China ta dakatar da mamaye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daya daga cikin tibiran China

Amurka ta bukaci China data gaggauta dakatar ci gaba da mamayen da take yi a tekun kudancin China da yake cike da takaddama.

Sakataren tsaron Amurka, Ash Carter ya shaida wa mahalarta wani taro kan sha'anin tsaro a Singapore cewa tabi'ar China a yankin ta sabawa yarjejeniyoyin kasa da kasa.

Ya ce kara girke sojoji da China take yi a tsibiran tekun zai iya ruruta wutar yaki.

Mista Carter ya ce a cikin watanni 18 da suka gabata, China ta mamayi yankin mafi girma da ya wuce wadanda sauran kasashen da take takaddamar da su suka mamaya.

Sakataren tsaron ya ce Amurka tana bukatar a warware takaddamar cikin lumana, a saboda haka yakamata dukkan kasashen dake wawason tsibiran tekun su dakatar da mamayen da sukeyi.