Wolfsburg ta lashe DFB Pokal a karon farko

Image caption 'Yan wasan Wolfsburg

Wolfsburg ta dauki kofin kalubalen Jamus na bana kuma a karo na farko a tarihi tun lokacin da aka kafa kungiyar.

Wolfsburg din ta cinye Borussia Dortmund ne da ci uku da 3-1 a karawar da suka yi a ranar Asabar.

Borussia Dortmund ta buga wasan ne da nufin yi wa kociyanta Jurgen Klopp wanda zai bar kungiyar a bana.

Borussia Dortmund wacce take da tarihin daukar kofin karo uke ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang.

Sai dai Wolfsburg ta farke kwallon ta hannun Luiz Gustavo, sannan Kevin De Bruyne ya kara ta biyu Bas Dost ya ci ta uku.

An kafa Wolfsburg a ranar 12 ga watan Satumbar 1945, kuma ta kammala gasar Bundesliga bana a mataki na biyu kan teburi.