'Yan Fansho sun kai Kwankwaso EFCC

Tsohon gwamnan kano Rabiu Musa Kwankwaso
Image caption Tsohon gwamnan kano Rabiu Musa Kwankwaso

Masu korafin sun zargi gwamnan da kin mika kudaden 'yan fanshon ga wani asusu da doka ta tanadar da kuma yin gaban kan sa wajen sarrafa kudaden 'yan fansho, ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

Takardar korafin ta ambato wasu sassan dokoki na kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar fansho ta Jihar Kano wadanda suka ce tsohon gwamnan ya yi musu karan tsaye wajen yin amfani da kudaden fanshon sabanin abin da doka ta tanada kamar yadda lauyan 'yan fanshon Barrister Audu Bulama Bukarti ya baiyana.

Bayan tsohon gwamnan kanon, takardar koken ta kuma hada da tsohon kwamishinan kudi na jihar kano da babban akanta na jihar da kuma kwamitin amintattu na asusun 'yan fansho.

To sai dai Jafar Jafar wani na hannun daman tsohon gwamnan ya musanta duk zarge zargen yana mai cewa ba a tsallaka hurumin doka ba wajen yin amfani da kudin.

Ya kara da cewa an yi amfani da kudi Naira biliyan 34 wajen gina gidajen kwankwasiyya, Amana da Bandarawo, biliyan hudu ne kacal na 'yan fansho a ciki, yana mai cewa ba laifi bane don an yi amfani da kudin domin yana cikin tsarin doka.