'Zan duba zargin Amnesty' - Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce zai duba zargin da kungiyar Amnesty ta yi na cewa sojojin Najeriya sun keta hakkin bil'dama.

Wani rohoto da kungiyar ta fitar a Abuja, babban birnin Najeriya, ya ce wasu manyan janar-janar na soja sun kawar da kai lokacin da kananan sojojin da ke karkashinsu ke cin zarafin jama'a a arewa-maso-gabashin kasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriyar, Garba Shehu ya fitar ta ce shugaban ya kadu matuka da jin rohoton wanda ya ce "mai matukar ta da hankali ne."

Sanarwar wadda aka fitar daga Yamai, babban birnin Nijar, inda shugaban ke ziyara yanzu haka ta kuma ce Shugaban Najeriyar ba zai yi wasa da maganar hakkin bil'adama ba, wanda ya ce ginshiki ne na tsarin domokradiyya.

Don haka zai tabbatar da cewa ya bi diddiggin maganar.

Sai dai rundunar sojin Najeriyar a nata bangaren ta ce zargin na Amnesty ba shi da tushe.

Amma kuma wani mazaunin garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno ya shaida wa shashen Hausa na BBC cewa akwai hujjojin da ke nuna cewa sojoji na cin zarafin jama'a.

Malam Husaini Monguna, ya ce ya kamata a kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa domin jin bahasin jama'a a kan zarge-zargen.