An fara nada jami'an gwamnati a Najeriya

Image caption Sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya fara nada jami'an gwamnati

A karon farko na nade-naden jami'ai a sabuwar gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shugaban ya sanar da nadin mista Femi Adesina tare da malam Garba Shehu a matsayin masu magana da yawun gwamnati, a ranar Lahadi.

Mista Femi Adesina wanda shi ne shugaban kungiyar editoci ta Najeriya kuma manajan darektan gidan jaridar The Sun newspapers, zai kasance a matsayin mai ba wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai.

Shi kuma malam Garba Shehu wanda ya kasance mai magana da yawun ofishin yakin neman zaben Muhammadu Buhari, ya zamo babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labaran.

Kazalika, shugaban kasar ya sanar da nadin malam Lawal Abdullahi Kazaure a matsayin babban mai kula da walwalar baki a fadar gwamnatin kasar.