'Ma'aikatan CBN sun sace naira biliyan 8'

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Jami'an CBN din sun shafe shekaru suna zambar kafin dubu ya cika

Hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa a Nigeria, EFCC, za ta gurfanar da wasu manyan jami'an babban bankin kasar gaban kuliya bisa zargin yin zambar kusan naira biliyan takwas.

Hukumar EFCC ta ce manyan jami'an bankin na CBN su shida tare da wasu jami'an bankunan 'yan kasuwa na kasar su 16 sun hada baki wajen yin zambar wadannan makudan kudaden ta hanyar sauya adadin wasu tsofaffin kudi da suke kula da su.

A cikin wata sanarwa, kakakin EFCC Wilson Owujaren ya ce za a gurfanar da wadannan mutanen su 22 gaban babbar kotun tarayya da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo.

A cewar EFCC jami'an na bankin CBN sun hada da Patience Okoro Eye, Afolabi Olufemi, Kolawole Babalola, Olaniran Muniru Adeola, Fatai Yusuf Adekunle da kuma Ilori Adekunle Sunday.

Mazambatan suna yin wata badakala ce ta tsofaffi da kuma yagaggun kudade a jihohi da dama na kasar.