Bam ya fashe a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Isa Gusau

Kwana guda bayan wani harin kunar-bakin wake da ya hallaka mutane a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a Najeriya, wani bam din kuma ya sake fashewa a birnin.

Mutane 8 ne aka ruwaito cewa sun mutu a lamarin da ya faru a tashar Baga da ke Maiduguri.

Ganau sun kuma ce bam din ya jikkata mutane da yawa.

Wani mazaunin birnin ya shaida wa shashen Hausa na BBC cewa "mun ji karar gaske da ya firgita mu lakacin da bam din ya fashe."

Ko a jiya ma wani dan kunar-bakin ya ta da bam a wata kwata a garin, kuma akalla mutane 13 ukku ne suka mutu a lamarin.