"Zamu rage ma'aikata 6,000"

Hakkin mallakar hoto Bombardier
Image caption Jirgin kamfanin Malaysia

Kamfanin jiragen sama na Malaysia wanda jiragensa biyu suka bace a bara, ya sanar da cewa zai rage ma'aikata 6,000 -- kimanin kashi daya bisa uku na ma'aikatansa.

Yayin da yake sanar da labarin, babban shugaban kamfanin dan kasar Jamus Christoph Mueller, ya ce kamfanin yana fuskantar karayar arziki.

A watan Maris din bara ne, wani jirgin Malaysia ya bata a hanyarsa ta zuwa birnin Beijing na kasar China daga Kuala Lumpur babban birnin Malaysia.

Watanni hudu bayan nan ne kuma wani jirgin kamfanin ya tarwatse a sararin samaniyar kasar Ukraine sakamakon harbo shi da aka yi da makami mai linzami.

Masu sharhi dai sun ce rashin tattali shi ne ginshikin matsalolin da kamfanin ke fuskanta.