An damke masu cin naman mutane a Oyo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda sun ce har yanzu suna gudanar da bincike

Rundunar 'yan sandan jihar Oyo da ke kudancin Nigeria ta gabatar da wasu mutane da ta ce suna cin naman dan adam domin yin tsafe-tsafe.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Alhaji Musa Muhammed Katsina ya shaida wa BBC cewa mutanen da aka kama suna dafawa, sannan su ci naman dan adam sannan kuma an tsinci kokon kawunan mutane a cikin gidan da ake zargi suna tsafi.

Kwamishinan ya kara da cewar mutanen da suke wannan tsafin suna kuma aikata damfara inda suka damfari mutane da dama a jihar ta Oyo.

Alhaji Muhammed Katsina ya kara da cewar 'yan sanda sun kuma damke wani mutumi wanda ke saduwa da 'ya'yansa mata su biyu da nufin yin tsafi.

Ko a cikin watan Maris ma, sai da rundunar 'yan sandan jihar ta Oyo ta kama wasu mutane bakwai bisa zarginsu da yin tsafi inda aka kama su da kawunan mutane, da kasusuwa a cikin wani gini da ba a kamalla shi ba a wata unguwa a Ibadan.