Jirgi mai amfani da rana ya tsaya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A watan Maris ne jirgi mai amfani da hasken rana ya fara zagaye duniya

Jirgin nan mai amfani da hasken rana wanda ya ke zagaye duniya yana fuskantar barazana sakamakon mummunan yanayi a yankin tekun Pacifik.

Jirgin ya taso ne daga kasar China kan hanyarsa ta yin tafiyar kwanaki shida zuwa Hawaii ta Amurka.

Tawagar masu hasashen yanayi na jirgin sun umarci matukin dan kasar Suwizalan da ya juyo da akalar jirgin zuwa Japan maimakon Hawaii har sai yanayin ya daidaita.

Jirgin -- wanda yake da dogayen fuka-fukai masu zuko hasken rana sannan yana da nauyi kwatankwacin nauyin mota, yana bukatar kyakkyawar iska saboda rashin gudunsa da kuma sararin samaniya mai haske domin ya samu zuko hasken rana.

Tun a watan Maris ne jirgin ya fara shawagi domin zagaye duniya inda ya tsaya a kasashe da dama kuma wasu matuka jirgi 'yan kasar Suwizalan ne su ke yin karbebeniya wajen tuka shi.