Ana cin zarafin kananan yara a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption 'Yan tawayen Syria

Wani bincike da BBC ta yi ya bankado yadda kungiyoyin 'yan tawayen Syria su ke cin zarafin yara kanana da kuma saka yara aikin soja.

Wani yaro ya bayyana cewa, an sa shi yayi yaki, kuma ya aikata kisa karkashin kungiyar Nusra Front da ke da alaka da kungiyar Al Qaeda.

A bidiyon yanka mutane da kungiyoyin tawayen Syria su ke fitarwa an sha nuna kananan yara.

Binciken ya nuna cewar ana daukar yara 'yan shekaru 12 a horas da su ka na kuma a tura su fagen daga.

An kuma gano mayakan IS su na nunawa kananan yara bidiyon yadda ake fillewa mutane kai, tare da ba su kwarin gwiwar su ma su aika irin hakan.