Matan da suka yi tsirara a Uganda

Wasu tsofaffin mata a wani kauye da ke kasar Uganda sun yi wani abu da al'ada ta yi Allah-wa-dai da shi domin nuna bacin ransu game da mallakar filaye, inda suka yi tsirara a gaban mutane.

Matan dai sun cire tufafinsu suka yi zigidir a gaban manyan jami'an gwamnati da sojoji da 'yan sanda da kuma daruruwan mutanen da ke yankin.

Sun fara da cire rigunansu inda daga bisani suka yaye zannuwansu da kuma fatarinsu baki daya.

Sun kuma ta yin ihu suna fadin "Lobowa, Lobowa!" a yarensu na Luwo wanda hakan ke nufin "Filayenmu, Filayenmu!".

Wasu daga cikinsu dai sun kasance a zaune a waje daya amma sun nuna goyon bayansu ga abin da sauran suke yi inda suke ta faman kururuwa.

Image caption Wasu daga cikin matan kuwa kururuwa suka dinga yi a wajen

'Tawagar Gwamnati'

Al'amarin, wanda ya faru sakamakon zargin cewa gwamnatin kasar na shirin korar su daga wasu filayen da suka gada kaka da kakanninsu, ya faru ne a kauyen Apaa da ke gundumar Amuru.

A ranar da al'amarin ya faru, ministocin gwamnati guda biyu sun isa garin tare da wasu masu safiyo domin shata iyakar filayen da matan da kuma sauran al'ummarsu ke rayuwa a wajen.

Amma sun girgiza da abin da suka gani.

A yayin da wani dan sanda ke daukar hotuna, sai daya daga cikin matan ta taho wajensa tana mirginawa a kasa sannan ta daga kafarta sama.

Ba shiri ya gudu ya bar wajen.

Image caption A kabilar Acholi idan mace ta yi tsiarara a gaban mutane hakan na nuna cewa tsinuwa za ta tabbata a kan makiyinsu

'Tsinuwa'

Fitowar mace gaban mutane tsirara na nufin wani babban al'amari a wajen mutanen Acholi da ke arewacin Uganda.

Sun dauki yin hakan wani al'amari mai karfi da ya fi yin fada saboda hakan na nuna cewa tsinuwa da lalacewa za su tabbata a kan duk wani makiyin matan.

Wannan rigimar filaye dai an kai kwashe kimanin shekaru goma ana yin ta.