Kotun Kolin Amurka ta goyi bayan Musulma

Hakkin mallakar hoto Getty

Kotun Kolin Amurka ta yanke hukuncin da ya goyi bayan wata mata Musulma, wadda wani kamfanin saida tufafi ya ki bai wa aiki a garin Tulsa a jihar Oklahoma.

Kamfanin, Abercrombie & Fitch, ya yanke shawarar kin ba da aiki ga Samantha Elauf, 'yan shekarar goma sha a shekarar 2008, bisa togaciyar cewa mayafin da ta sa a ka a lokacin tattaunawa da ita, ya saba wa manufar kamfanin a kan irin shigar da ta kamata ma'aikatan kamfanin ya yi.

Hukumar Amurka Mai Kula da Ba da Dama Bai Daya ga Kowa ita ce ta shigar da karar a madadin ita Samantha Elauf din.