Babu Shekau a sabon bidiyon Boko Haram

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Babu wanda ya san abin da ya faru da Shekau

Kungiyar ta Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo inda take musanta cewa, an fatattaki mayakanta daga dajin Sambisa.

An dai dade ba a ga wani bidiyo daga kungiyar ba, inda a baya aka saba ganin jagoran kungiyar Abubakar Shekau yana fitowa yana magana.

A wannan karon, wani mutumi da bai gabatar da kansa ba ya ce dakarun kawance na kasashen Kamaru da Chadi da Nigeria da kuma Nijar ba su samu galaba a kan kungiyar ba.

Babu wanda ya san abin da ya faru da Abubakar Shekau.

A bidiyon wanda aka wallafa a shafin YouTube dauke da tambarin 'kungiyar IS a yammacin Afrika' mai tsawon mintuna 10, an nuna wasu mutane da mayakan Boko Haram suka kashe.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da bam ya hallaka mutane da dama a kasuwar shanu da ke Maiduguri inda wasu rahotanni ke cewa, mutane akalla 20 sun mutu.

Sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce shalkwatar tsaron kasar za ta koma Maiduguri domin murkushe ayyukan Boko Haram.