Kamfanin taba zai biya diyyar dala biliyan 12

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Akwai dumbin mashaya sigari a Canada

Wata Kotu a lardin Quebec da ke kasar Canada ta umarci wasu kamfanoni uku na taba sigari su biya wasu mashaya tabar sama da dala biliyan 12 a matsayin diyya, saboda ambaton da suka yi cewar ba a gargade su ba a kan hadarin da ke tattare da shan tabar sigari.

Wannan kara da aka shigar -- wadda ita ce mafi girma a tarihin shari'a a kasar ta Canada, an shigar da ita ne a madadin mutane sama da miliyan daya.

An wakilci bangarori biyu ne a shari'ar -- daya daga cikin su na mutanen da suka ce sun kamu da rashin lafiya ne mai tsanani sakamakon shan taabar da kuma daya rukunin mutanen da ke cewar tabar ta shiga ransu, kuma ba sa jin za su iya dakatar da shan ta.

Kamfanonin uku dai, sun yi shirin daukaka kara.