Aikin ceto a jirgin ruwan China

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wankin hula na neman kai masu aikin ceto dare

Masu aikin ceto a China na can suna kokarin neman sama da mutane 400 da wani jirgin ruwa da ya kife da su a kogin Yangtze.

A halin da ake ciki dai yawan mutanen da aka ceto bai taka kara ya karya ba, bayan huda wani bangaren jirgin, lokacin da aka ji wasu daga cikin fasinjojin na neman a kai musu dauki.

An dai tsare keptin din jirgin ruwan da kuma babban Injiniya mai kula da shi, wadanda suka tsira.

Sun bayyana cewa wata guguwar ruwa ce ta kifar da jirgin, kuma jirgin bai nuna wata alama ko siginar nema taimakon gaggawa ba kafin ya nutse.

Dangin Fasinjojin da hadarin ya ritsa da su dai sun taru suna so su san makomar 'yan uwansu.