An rantsar da Al-Bashir a Sudan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Sudan Omar al-Bashir

An rantsar da shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir wa'adin mulki na shekara biyar bayan nassarar da ya samu a zaben da aka gundanar a watan Afrilu.

Shugaba al-Bashir, wanda kotun hukunta manya laifuka ta duniya ke tuhuma da laifukan yaki a Darfur, ya lashe zaben da kuri'u sama da kashi casa'in da hudu a cikin dari.

Rashin fitar jama'a dayawa da kuma kin shiga zaben da wasu jami'un adawa suka yi ya rage armashin zaben.

Shugabanin Masar da Zimbabwe da kuma Kenya duk sun halarci bikin rantsar da shugaba Al-Bashir din.

Shugaba Al Bashir dai na mulkin kasar Sudan ne tun 1989, bayan wani juyin-mulkin da ya yi.