Ana zaman zullumi a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Rugugin fashewar abubuwa masu kara ya jefa birnin Maiduguri a halin dimuwa

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, na cewa mazauna birnin suna cikin halin zulumi sakamakon rugugin fashewar abubuwa masu kara a birnin.

Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa da misalin karfe 12:30 na daren Talata ne aka fara jin fashewar abubuwan masu kama da bama-bamai.

Sannan kuma sun ce suna ganin haske yana tashi a sama duk da cewa dai ba su iya tantance ko hasken yana sauka a wani wuri ne ba.

Al'amarin dai ya jefa mutanen cikin garin na Maiduguri cikin halin dimuwa, a inda wasu suka bar gidajensu suka shiga gari.

Sai dai kuma an ce an daina jin rugugin tun bayan da wani jirgi ya yi shawagi a birnin da misalin karfe biyun daren na Talata.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan abin da ya faru.

Sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce shalkwatar tsaron kasar za ta koma Maiduguri domin murkushe ayyukan Boko Haram.