Bam ya hallaka mutane a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Isa Gusau
Image caption Harin bam din da aka kai 'yan watannin da suka wuce a Maiduguri

Wani abu da ake zaton bam ya fashe a kasuwar shanu da ke birnin Maiduguri a jihar Borno inda mutane da dama suka hallaka.

Bayanai sun ce wata mata 'yar kunar bakin wake ce ta tayar da bam din a lokacin da mutane ke hada-hada a cikin kasuwar.

Kawo yanzu babu bayanai a hukumance na adadin wadanda suka rasu.

Hakan na zuwa ne bayan da aka kwana cikin zullumi a Maiduguri sakamakon jin karar fashewar abubuwa da ake zargin Boko Haram ne suka harba.

A karshen makon da ya wuce, an hallaka mutane fiye da 30 a jihohin Yobe da Borno a wasu har-haren bam.

Sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce shalkwatar tsaron kasar za ta koma Maiduguri domin murkushe ayyukan Boko Haram.