Sankarau ta hallaka mutane 545 a Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana karancin allurar riga-kafi a Afrika

Annobar cutar sankarau da ta barke a jamhuriyar Nijar ta hallaka mutum 545 kamar yadda hukumar lafiyar ta duniya- WHO ta sanar.

A cewar hukumar, mutane fiye da dubu takwas ne suka kamu da cutar kuma lamarin na kara muni saboda karancin allurar riga-kafi.

Kakakin WHO, Cory Couillard ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa adadin wadanda suka kamu da cutar ya fi muni a cikin tsakiyar watan Mayu inda mutane 132 suka rasu sannan wasu fiye da dubu biyu suka kamu da ita.

Hukumar lafiya da duniya- WHO ta ce tun daga watan Janairu zuwa Afrilun bana, sankarau ta yadu a kasashen Nigeria da Ghana da kuma Nijar inda ta hallaka mutane 910 a yayin da mutum fiye da dubu 11 suka kamu da ita.

Cutar sankarau ta zama gama-gari a lokacin rani a wasu kasashen Afrika inda ta hallaka mutane fiye da 20,000 shekarar 1996 zuwa 1997 lokacin da ta zama wata babbar annoba.