Ba ni da ko dala daya a waje - Nyako

Image caption Tsohon gwamnan jihar Adamawa a Najeriya, Murtala Nyako

Tsohon gwamnan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, Rear Admiral Murtala Nyako mai ritaya, ya ce bai mallaki ko da dala daya ba a kasashen duniya.

Ya kuma kalubalanci duk masu zarginsa da ta'annati da kudaden gwamnati da su bujuro da wata shaida da za ta nuna hakan.

Tsohon gwamnan dai ya kara da musanta rahotanni da suke cewa neman da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta kasa wato EFCC, ta yi masa ne yasa ya bar kasar a bara. Ya dai ce barazanar kisa ce ta sa shi yin hijira.

Nyako ya ce ya je hukumar ta EFCC domin jin neman da suke yi masa, a inda suka sallame shi da cewar za su sake neman sa a gaba.