'Za mu ci galaba a kan Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto STATE HOUSE TWITTER
Image caption Nijar ce kasa ta farko da Buhari ya ziyarta a matsayin sabon shugaba

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya bayyana kwarin gwiwa cewa dakarun kasar za su murkushe 'yan Boko Haram.

A jawabinsa lokacin da ya ziyarci Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar a birnin Yamai, Shugaba Buhari ya ce sojojin Nigeria na da karfin da za su kawo karshen ayyukan masu ta da kayar baya.

Buhari ya ce "Muna duba wasu hanyoyi ta yadda za mu sauya salon yaki da Boko Haram."

Ana shi bangaren, shugaba Issoufou ya ce matakin gwamnatin Nigeria na mayar da cibiyar dakarun kasar zuwa Maiduguri zai taimaka wajen kawo karshen ayyukan Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria a yayinda wasu da dama suka rasu a Nijar da Kamaru da kuma Chadi.