Issoufou ya tarbi Buhari a Yamai

Hakkin mallakar hoto STATE HOUSE TWITTER
Image caption Shugabannin kasashen Najeriya da Nijar, Muhammad Buhari da Mahammadou Issoufou

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya soma wata ziyarar aiki zuwa jamhuriyar Nijar mai makwabtaka domin tattauna yadda za a yaki kungiyar Boko Haram.

Ziyarar ita ce ta farko da sabon shugaban na Najeriya zai kai wata kasa tun bayan kama aiki kasa da mako guda.

Buhari ya isa Yamai babban birnin kasar inda ya gana da shugaba Mahammadou Issofou a fadar gwamnati.

Shugabannin kasashen biyu sun sha alwashin hada kai kan sha'anin tsaro musamman yadda za a dakile hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Hare-haren 'yan kungiyar ta Boko Haram dai suna kara kamari a kasashen biyu musamman a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da suka da mata da kananan yara.