Kulle saboda cutar Ebola a Liberia

Image caption Rayuwar Joseph da Josephine ya sauya sosai tunda mahaifiyarsu ta kamu da cutar Ebola.

Siannie Beyan ta na tsaye cikin taron wadanda suka tsira daga cutar Ebola a wani dakin taro a Monrovia babban birnin Liberia, tana 'yar wake-wakenta da murmushin farin ciki.

An yi nasarar dakile cutar a Liberia, ba a samu wanda ke dauke da kwayar cutar ba kwanaki 10 kenan, kuma mutane sun samu sauki sosai.

Wannan 'yar karamar kasar ta fara samun saukin halin wariya da karayar tattalin arziki da ta shiga a watanni da suka gabata.

Mutane na da kyakkyawar fata duk da halin ha'ula'i da kasar ta shiga.

"A firgice mu ke" In ji mataimakin Ministan kudi, James Kollie.

"Cutar Ebola ba ita ce kadai dalilin shiga wannan hali da muka yi ba, amma yaduwarta ta fito da gazawarmu da karayar tattalin arzikin da kasar ta shiga".

Image caption Siannie (ita ce ta farko a hannun dama) tare da makwabtanta. Kullum cikin hijira ta ke a watannin da suka gabata.

'Kadaici'

A bara, Siannie ta na aikin kasuwanci ne a Monrovia, inda take sayar da 'yan kayan kwadayi da man goge baki a cikin amalanke, ta na ribar kusan dala 160 a kowane wata.

Cikin rufin asiri ita da mijinta ke biyan kudin hayan gida kuma su biyan kudin makarantar yara.

An kwantar da Siannie a ranar 27 ga watan Agusta, a asibitin kula da masu cutar Ebola, watau ELWA 3 Ebola Treatment unit da ke garin, wanda ke karkashin kulawar Medecins Sans Frontieres.

Siannie ta samu sauki bayan wata daya, amma da ta dawo gida, maigidanta ya ce baya bukatar daga ita har yaran.

"Ya ce baya sona kuma don na kamu da Ebola. Baya bukatar "matar da ke da cutar Ebola". Na shiga wani hali na kadaici," In ji Siannie.

Image caption An bude makarantu da dama yanzu a Liberia, amma yaran Siannie basu koma ba saboda rashin kudi.

Image caption An fara gwajin alluran rigakafin cutar Ebola a Liberia.

'Rayuwa a boye'

An sami Siannie a wani daki a garin Paynesville wanda ke wajen Monrovia.

Wannan shi ne wuri na uku da ita da yaranta suka canza tun watan Satumba.

A sassanyar murya Siannie ta ce, "Ina hijira idan mutanen da nake zaune da su suka gano na taba kamuwa da cutar Ebola. Sai su ce basu bukatar zama na a gidansu. Kullum cikin boyo nake."

Ta yi bayanin cewa "Ina yi wa yara na gargadi da: kar su gaya wa kowa cewa mahaifiyarsu ta kamu da cutar Ebola a da. 'idan kuka gaya masu toh dole mu sake canza wurin zama'.

"Toh yaran ba sa gaya wa kowa har yanzu. Ba na so in sake tashi domin bani da kudi".