Matasa sun kashe dan sanda a Gombe

Hakkin mallakar hoto gombe government
Image caption Gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Dankwambo

Rahotanni daga jihar Gombe a Najeriya, sun ce a ranar Talata wasu matasa suka yi wa wani jami'in dan-sanda duka har suka kashe shi, bayan da suka zarge shi da bindige wani matashi farar hula har lahira.

Kashe-kashen sun biyo bayan wani hadari ne da aka samu tsakanin wani farar hula mai tafiya a KEKE NAPEP da kuma 'dan-sandan wanda ke tafiya kan babur, amma lamarin ya rincabe daga bisani.

Kawo yanzu dai kura ta lafa kuma hukumomin tsaro na cewa sun kaddamar da bincike kan faruwar lamarin.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya musanta zargin cewa da gangan dan sandan ya yi harbin.