"Za mu mai da 'yan tawaye saniyar ware"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu tayar da kayar baya a Mali

Shugaban Nijar Muhammadu Isufu, da takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande, sun yi kira ga manyan kungiyoyin 'yan tawayen kasar Mali su gaggauta sa hannu kan shirin wanzar da zaman lafiya da aka cimma a kasar Algeria.

Shugabannin na Nijar da Faransa sun yi wannan kiran ne a ranar Talata, lokacin da shugaban na Nijar Muhammadu Isufu ya gana da takwaran nasa na Faransa a birnin Paris.

Muhammadu Isufu ya ce "Dole mu matsa musu lamba su sanya hannu ta yadda za mu samu a mayar da masu tsattsauran ra'ayin addini saniyar ware."

Kazalika shugabannin sun yi kira ga kasashen yankin sahel da su karfafa huldarsu domin dakile kungiyar Boko Haram.

A watan da ya gabata ne gwamnatin Mali da wasu kungiyoyin 'yan tayar da kayar baya da kungiyoyin kasa da kasa suka sa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Amma manyan kungiyoyin 'yan tawayen kasar suka bujire wa yin hakan.