An fara gyaran birnin Berbera

A baya, Berbera wanda ke kan ruwan Aden wanda ke makwabtaka da Yemen cibiyar cinikayyar harkokin ruwa ne tsakanin kaseshen cikin Afrika da kaseshen tsakiyar gabas.
Bayanan hoto,

A baya, Berbera wanda ke kan ruwan Aden wanda ke makwabtaka da Yemen cibiyar cinikayyar harkokin ruwa ne tsakanin kaseshen cikin Afrika da kaseshen tsakiyar gabas.

A da Berbera da ke wani yanki a Somalia, gari ne da ke samun ci gaba a harkar kamun kifi. Amma a yanzu yana neman durkushewa, in ji James Jeffrey.

Bayanan hoto,

Wata tashar jiragen ruwa da ke makwabtaka da Djibouti ta mamaye cinikayya wanda hakan ya rage damar da Berbera ta ke da ita a harkar cinikayya.

Bayanan hoto,

A tsakiyar garin, inda ake kamun kifi, duk lalatattun jiragen ruwa ne suka warwatsu a ko'ina sannan da wasu jirage ma wadanda suka fara nutsewa wanda hakan ya nuna cewar garin ya rasa kadara.

Bayanan hoto,

Kasaitattun gine-gine marasa kwari na Berbera wadanda suka hada da manya-manyan gidaje na lokacin Ottoman inda 'yan kasuwarLarabawa da Indiyawa da kuma yahudawa suka taba zama na rarrabuwa.

Bayanan hoto,

A da Somaliland na karkashin ikon Biritaniya, har sai da ta samu 'yancin kai a shekarar 1960, duk da cewar har yanzu akwai ragowar abubuwa kadan da suke tunasar da mulkin mallaka.

Bayanan hoto,

Tatalin arzikin Somaliland ya dogara ne a kan fitar da dabbobi daga karamar tashar jirgin ruwa da ke Berbera. Ana aike Akuwowi da Rakuma Saudiya yayin da ake sayarwa da kasar Ethiopia da ke makwabtaka da ita kashi sabin cikin dari na abubuwan da ake shigo da su.

Bayanan hoto,

Wali Daud daga Ma'ikatar da ke kula da harkokin kudaden Somaliland ya ce "A baya Somaliland cibiyar kasuwanci ce mai muhimmanci. A yanzu gwamnati ta na neman kasashen waje su zuba jari a tashar jirgin ruwan".

Bayanan hoto,

Tarayyar ma'aikatan bakin teku na Somaliland suna taruwa a tashar ko zasu samu aiki. Sun yi korafi a kan cewa ba'a biyan su albashi iri daya. Ana biyan su kusan dala 250 a wata, amma ma'aikata daga kasashen waje suna karbar fiye da haka, saboda basa cikin kungiyoyin kasashen duniya da aka sani.

Bayanan hoto,

Gabar tekun Somaliland da ke da tsawon kilomita 850 zai iya kasancewa wani wuri da za'a iya habaka kasuwancin kifi. Yanzu haka masunta kalilan ne ka wai suke a wuraren da suke kewaye tekun.

Bayanan hoto,

Wasu sun ba da shawarar amfani da bakin teku da ba'a gano ba domin jawo hankalin masu yawon bude ido. Sai dai Gogena Jameson, wata ma'aikaciyar kamfanin Duniya Strategy da ke bai wa masu yawon bude ido shawara, ta ce babu isassun kayayyakin more rayuwa. Duk da cewar yankin yana daga cikin abin da ke kara kawun wuri, ba tabo wannan bangaren ba. Wasu sun ce kamar yadda kasar Masar take ne a baya kafin ta samu bunkasa a harkar yawon bude ido.

Bayanan hoto,

Babu zirga-zirga da ke wakana a shagunan sayar da kifi a Berbera. Ma'aikata matasa suna zuwa Hargeisa, babban birnin Berbera domin yin aiki saboda 'yan Somaliland da suka kai minzalin yin aiki basu da aikin yi.

Bayanan hoto,

Mutane suna cin ganye khat ne saboda debe lokaci, abin da aka kimanta kashi 90 na mazan Somaliland ke yi.

Bayanan hoto,

A iya sannin Jama Musse, darakta a cibiyar kula da harkokin al'adu a Hargeisa, ta ce babu wani shirin da ake yi na gyara yanayin abubuwa kuma abin takaicin shi ne dole su dauki mataki nan kusa idan dai har suna so su kare ta daga durkushewa.